Batutuwan da suka ja hankalin jaridun Jamus
February 3, 2023Jamusawa sun ji takaicin aikin Mali, wannan shi ne taken Jaridar Die Welt, wadda ta ce 'yan gudun hijira na neman kariya daga sojojin Jamus na Bundeswehr a Gao. Amma sojojin sun makale a sansaninsu. Gwamnatin Tarayya Jamus kuma ta zuba ido kan wannan tirka-tirka tsakanin Mali da sojojin kasashen waje. Die Welt ta ruwaito cewa yanzu akwai sama da mutane 100,000 a wasu masu lura da al'amura na ganin mutane 200,000 ne ke cikin halin bala‘i a sansanonin da ke wajen birnin na Gao, kuma kullum sai an kawo sabbin 'yan gudun hijira masu tserewa daga hare-haren 'yan ta'adda.
Jaridar ta Die Welt ta yi sharhinta kan karin karbuwa da kasar Rasha ke samu a yammacin Afirka. Tana mai cewa korar Faransa ta bai wa Rasha kyauta. Bayan Afirka ta Tsakiya da Mali, sojojin Faransa ala dole ne su tattara nasu su fice daga kasar Burkina Faso. A wulakance gwamnatin Paris ta fidda sanarwar kan abin da a baya ta ce yaki da ta‘addanci a yammacin Afirka.
Wani zane mai ban dariya ya karade shafukan sada zumunta na Burkina Faso, wanda ke nuna Faransawa a matsayin mugayen ‘yan mulkin mallaka da kuma sojojin haya na Wagner na Rasha a matsayin mataimaka na abokantaka, sakamakon yakin da aka kwashe tsawon shekaru ana yi da ta'addancin masu ikirarin Jihadi a yankin Sahel na iya zama babban koma baya domin a ta fuskar Afirka, kawai Paris ta gaza.
A wani abu da ya shafi Rasha da Afirka, Jaridar Die tagszeitung ta ce Rasha, mai farinjini a Afirka. Jaridar ta cigaba da cewa Rasha na kara yin tasiri a fagen yada labarai a Afirka, inda ta yi nasarar yada manufofinta, kuma tashoshinta na yada labarai da ma horar da 'yan jarida da dama na Afirka. Babban misali dai shi ne yarjejeniya a ma'aikatun harkokin waje na Rasha da Uganda, ya kamata a gayyaci 'yan jaridar Uganda zuwa kwasa-kwasan horo a babban ginin gidan rediyon kasar Rasha a birnin Moscow. Bugu da kari, Uganda za ta ba da mitoci don watsa shirye-shiryen Turanci na gidan talabijin na Russia Today a Uganda. Jaridar ta ce Kamfanin dillancin labaran Rasha, wanda ya hada da gidan rediyon kasar Sputnik, yana aiki kafada da kafada da kafafen yada labaran kasar Uganda.
Jaridar Welt am Sonntag buga labarinta kan kasar Habasha, inda ta fara karin magana tana mai cewa, Tsakanin kiyayya da gafara. Yankin Tigray a Habasha ya kasance wurin da aka yi kisan gilla mai yawan gaske. Jaridar ta ce kasashen Yamma sun dade da kawar da ido kan yakin, a yanzu gwamnatoci a Berlin da Brussels da Washington, duk sun damu ba don yawan kisan fararen hula ba, ba kuma sun damu don yawan karuwar yunwa ba, amma kasashen hankalinsu ya fara tashi ne saboda kasar Rasha ta fadada tasirinta a Afirka, kuma kasar Habasha na daya daga cikin wadanda ke karfata wajen Rasha.
Frankfurter Allgemeine Zeitung, cewa ta yi Hadiya madaci don sulhu da Maroko. Tsawon hutun ya kai shekaru takwas. Amma a karon farko tun shekarar 2015, jirgin gwamnati ya tashi daga Madrid zuwa Rabat da yammacin Laraba. A cikin jirgin akwai Firaminista Pedro Sánchez da ministoci goma sha biyu. A Madrid an yi ta maganar wani taro na tarihi na kwanaki.
A wannan Alhamis aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyin biyu masu kyau bayan fahimtar junar gwamnatocin Moroko da Spain. Hotunan daga babban birnin Maroko an yi niyya don nunawa duniya cewa babban rikicin ya kare daga karshe, kuma ba za a sake maimaita shi ba. A Rabat, gwamnatin Spain tana son yin amfani da sabon tsari don aza harsashin hadin gwiwa da makobciyarsu a yammacin tekun Bahar Rum.
Süddeutsche Zeitung: Aljeriya da Maroko da Tunisiya, sun kasance wuraren mafaka ga bakin haure daga yammacin Afirka. Jaridar ta ba da misali cewa a kan hanya tare da mai gyaran gashi Christine Bela a sabon gidanta da ke Tunis, ake samun tashin hankali tsakanin bakin haure da mazauna yankin.
Matar mai shekaru 32 da haifuwa daga Ivory Coast, tana yin bulaguron kwana shida a mako daga gundumar La Soukra, zuwa tsakiyar Tunis, ga shi kuma karuwar talauci a Tunisiya na yaduwa, kuma kyamar baki, musamman bakaken fata, matar ta ce mummunan kamanni ko kalaman batanci a bainar jama'a sun karu sosai a cikin shekaru hudun da ta yi a Tunisiya.