WasanniJamus
Bayern Munich ta yi wa Hoffenheim cin kaca
September 20, 2025
Talla
Harry Kane na Bayern Munich shi ne ya yi ruwan kallaye a ragar Hoffenheim da ke kasancewa masu masaukin baki. A nata bangaren kuwa dan wasan Hoffenheim Vladimir Coufal shi ne ya zura kwallo daya tilo a ragar Bayern Munich. A wannan kakar Kane ya zura kwallaye 13 ciki har da guda takwas a wasannin Bundesliga hudu.
Karin bayani:Bayern ta yi nasara a fitowar farko a Champions League
A sauran wasannin da aka fafata a wannan yammaci Freiburg ta lallasa Werder Bremen 3-0, yayinda Mainz ta doke Augsburg 4-1.