Bayern Munich tana kara karfi a Jamus
February 23, 2026
A gasar Bundesliga ta Jamus inda aka yi gumurzu tare da cin kwallaye daya-daya har guda 33 a wasannin da aka fafata a mako na 23.
An yaye labulen makon a ranar Jumma'a inda Mainz ta yi canjaras 1-1 a wasan da ta karbi bakuncin Hamburg.
Galibin wasannin sun gudana a maraicen Asabar inda Wolfsburg ta yi maraicen kure a gidanta bayan ta tashi wasa tana da ci 2 Augsburg na da ci 3,
Hoffenheim ta taka wa FC Köln birki a gidanta inda suka tashi ci 2-2, da kyar da jibin goshi B.Dortmund ta tsira da maki daya a ziyarar da ta kai wa RB Leipzig inda suka tashi wasa ci 2-2.
Gawo ya kusa juyewa da mujiya a fafatawar Bayern Munich da Frankfurt inda saura kiris Frankfurt din ta farke kwallaye 3 da ake binta bayan zura kwallaye 2 a mintuna na 77 da na 86. To amma yaya babbar ta rike wuta tare da dakile kwadayin Frankfurt inda aka tashi wasa 3-2.
Sai dai al'amura sun sukurkucewa Bayer Leverkusen wadda ta sha kashi ci 1-0 a ziyarar da ta kai wa Union Berlin. A sauran wasannin na mako na 23 na Bundesliga ta bana a jiya Lahadi Freiburg ta doke Mönchengladbag ci 2-1. St Pauli ta lallasa Weder Bremen ci 2-1 sai kuma Heidenheim da ta yi canjaras da Stuttgart ci 3-3.
Har yanzu Bayern Munich ce saman teburi da maki 60 yayin da mai biya mata Durtmund da ta yi barin maki a gidan RB Leipzig ke da 52, lamarin da ke nuna ratar maki 8 a tsakanin su.
Hoffenheim na a matsayi na 3 da maki 46, Stuttgart na biya mata a matsayi na 4 da maki 43 sai RB Leipzig da Bayer Leverkusen da ke a matsayi na 5 da na 6 da maki 41 da 39.
'Yan baya da dangi sun hada da St Pauli a matsayi na 16 da maki 20, sai Weder Bremen a matsayi na 17 da maki 19 sai kurar baya Heidenheim da ke ciki hadari inda take a matsayi na 18 da maki 14 kacal.
Wasannin Spain
A Spain ta leko ta koma wa Real Madrid bayan da Barcelona ta karbe jan ragamar teburin Laliga daga hannuta a wasannin mako na 25 da aka fafata a karshen makon jiya.
'Yan farin gidan sun karbi kida a hannun Osasuna ci 2-1 a ranar Asabar inda dan wasa Raul Garcia ya ci kwallo ta 2 mai matukar ban shawa a minti na 90 na fafatawar.
Ita kuwa Barcelona raga-raga ta yi da Levante a filin wasa na Nou Camp ci 3-0 a jiya Lahadi, lamarin da ya bai wa tawagar ta Hansi Flick damar darewa kan teburi da maki 61 inda ta shiga gaban Madrid da maki 1.
Ita kuwa Villareal da ta doke Valencia ci 2-1 na ci gaba da rike matsayi na 3 da maki 51, yayin da Atletico de Madrid ta karkare a matsayi na hudu da maki 48 duk da nasarar da ta yi a kan Espagnol da Barcelone ci 4-2, Betis Seville na rike da matsayi na 5 da maki 42 bayan ta gamu da turjiya daga Rayo Vellecano inda suka tashi kunnen doki 1-1.
Yadda ta kaya a Ingila
A Ingila Arsenal na ci gaba da zama daram kan teburin Pirimiya da maki 61 bayan iske Tottenham har gida ta yi mata yankan kauna ci 4-1 a wasan mako na 27.
Sai dai tawagar ta Arteta na shan matsin lamba daga Manchester City da ke a matsayi na 2 da maki 56 bayan doke Newcastle ci 2-1 amma kuma tana da kwantan wasa guda. Aston Villa na a matsayi na 3 da maki 51 duk da canjaras da ta yi da Leeds United ci 1-1.
Chelsea na rike da matsayi na 4 na wucin gadi da maki 45 bayan ta yi canjaras da Burnley a gida ci 1-1, saboda Manchester United da ke a matsayi na 5 ita ma da maki 45 na iya sabkota kasa domin tana da kwantan wasanni biyu inda a daren yau za ta yi tattaki zuwa Everton. Sai dai al'amura na kara jagulewa Liverpool inda take a matsayi na 5 da maki 45 duk nasarar da ta yi a gidan Nottingham Forest ci 1-0 sannan kuma tana da kwantan wasa guda.
A Najeriya an bude karo na biyu na gasar wasanni ta matasan jahohi 9 na yankin Niger Delta wadda ake kira Niger Delta Games. Za a kwashe mako guda cur ana fafata wannan gasa da aka fara tun daga ranar jummar da ta gabata.
Kammala wasannin Olympics
An kammala wasannin Olympics na Hunturun 2026 a Italiya inda tawagar Amurka ta lashe lambar zinarenta ta 116 a kwallon Gora na kankara bayan doke Canada.
Kasar Norway ce ta zo ta farko a jerin kasashen da suka fi samun lambobi yabo inda ta yi awon gaba da lambobi 41 tare shiga gaban Amurka da Netherland.
Sai dai a karon farko an samu wakilci daga yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara a wasannin na Olympics na hunturu, inda matashi Nathan Tchibozo, mai shekaru 21 ya wakilci Jamhuriyar Benin a wasan zamiyar kankara tare da tabbatar wa duniya cewa sha'awar wasanni ba ta da iyaka.
Nasororin da Italiya ta samu wajen shirya wasannin na 2026 kama daga gina sabbin filaye zuwa nisadi da annashuwa da mamaye biranen da suka karbi bakuncin gasar za su kasance babban kalubale ga Faransa wace a mika wa tutur karkar bakuncin wasannin na Olympics na huntun 2030.