1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Bayern ta yi nasara a fitowar farko a Champions League

September 18, 2024

A gasar zakarun nahiyar Turai, Bayern Munich ta lallasa Dinamo Zagreb na Croatia da ci 9-2. Harry Kane ya zura kwallaye 4 a ragar Dinamo yayin da sabon dan wasan da Bayern ta sayo Michael Olise ya zura kwallaye 2.

'Yan wasan Bayern Munich sun yi farin cikin bayan da suka doke Dinamo Zagreb
'Yan wasan Bayern Munich sun yi farin cikin bayan da suka doke Dinamo ZagrebHoto: Peter Kneffel/dpa/picture alliance

Stuttgart ta nan Jamus da ta fito da karfinta a shekaru 15 a Champions League ta yi rashin nasara a hannun mai rike da kambun zakarun nahiyar Turai Real Madrid da ci 3-1. Tsohon dan wasan Stuttgart Antonio Rüdiger shi ne ya zura kwallo na biyu.

Karin bayani: Bayern Munich ta yi wa Bochum cin kaca

A bangaren wakiliyar Italiya kuwa, AC Milan ta yi rashin nasara a hannun Liverpool da ci 3-1 a wasan da aka fafata a San Siro. Aston Villa ta lallasa Young Boys na Switzerland da ci 3-0 yayin da Sporting Lisbon ta lallasa Lille da ci 2-0.