1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar sadarwa ta Nijar na kokarin samar da dai-daito

Abdoulaye Mamane Amadou /LMJAugust 5, 2015

A Jamhuriyar Nijar hukumar sadarwa ta kasar CSC ta kaddamar da wani jadawalin ba wa kowa damar yin kamfe a kafafen yada labaran kasar.

Yahouza Sadissou Mabobi ministan sadarwa na Nijar
Yahouza Sadissou Mabobi ministan sadarwa na NijarHoto: DW/M. Kanta

A karkashin wannan sabon matakin dai za a ba wa jam'iyyun siyasa da ma 'yan takara damar shiga kafafen yada labarai na gwamnati da masu zaman kansu domin kawo karshen duk wasu rigingimmu da ake samu a lokutan yakin neman zabe. Dama dai hukumar ta CSC na sanya idanu da kuma jan hankalin kafafen yada labarai na gwamnati da masu zaman kansu da. Hasali ma wannan batun na matsayin wanda ake tsananin bukata a halin yanzu a yayin da Nijar din ke shirin shiga zabubbuka inda 'yan siyasa na jam'iyyun hamayya da masu mulki ke nuna zumudi wajan samun 'yancin yada manufofi da akidodinsu irin na siyasa a kafafen yada labaran gwamnati da masu zaman kansu.

Seini Oumarou shugaban jam'iyyar MNSD mai adawa a NijarHoto: MNSD

Kokarin tabbatar da adalci


Domin shimfida adalci na ba wa kowa wannan damar ne hukumar ta CSC ta kirkiro wani jadawali mai shirin rarraba lokutan magana a kafafen yada labaran ga 'yan takarar zaben shugabancin kasa da na 'yan majalisun dokoki da kuma na kananan hukumomi da hukumar zaben kasar ta ce za'ayi a cikin watan Mayun shekara mai zuwa. Alhaji Shu'aibu Mamane daya ne daga cikin mambobin hukumar sadarwar ta CSC


Ya ce: "A cikin kundin tsarin mulkin kasa su kafafen yada labarai na gwamnati dole ne suyi aikin kasa da manufofi na kasa su kuma masu zaman kansu dole su yada duk wasu manufofin da 'yan kasa suke so ba wai abin da wata jam'iyya take so ba, to lalle su masu zaman kansu ne don haka ba mu da wani dole na takura musu amma zamu tabbatar da cewa dole ne idan har wani ya na son ya shiga cikin wadannan kafafen yada labarai zai iya shiga ba tare da an hana mishi shiga ba.


Watsi da dokokin daga 'yan adawa

Mohamed Bazoum shugaban jam'iyya mai mulki PNDSHoto: DW/T.Mösch


Sai dai tun kafi a kai ko ina tuni bangaren jam'iyyun adawa sukayi fatali da matakin tare da cewa daman sun jima da suke jimirin wani babban rashin adalci na hukumar da ke hada baki da bangaren masu mulki ana yi musu. Injiniy Rabilu Alhaji Kane shi ne sakataren yada labarai na jam'iyyar MNSD nasara mai adawa ya kuma ce:

"Duk ungulu da kan zabuwa ne duk wanda za ka tambaya ko da ba dan siyasa bane zai gaya maka cewar yaudara ce kawai saboda wata kila suna neman wasu kayan aiki ko kuwa wata kwalliya ce ake son yi wa Turawa domin samun wani abu nan da watanni uku ko shida ko takwas amma dai banza ba ta makaho kuma a gaba za ka gani."

Sai dai batun ya sha banban a bangaren kawancen jam'iyyun da ke mulki inda sakataren yada labarun PNDS Tarayya ya ce sun gamsu da matakin da hukumar CSC ke shirin dauka, kana sakataren ya musanta kalaman na 'yan adawar.

Ya ce "Kai su abin da suka saba da shi kullum sharri ne anyi kara anyi itace alhali kuwa 'yan Nijar kansu ya waye."

Tuni dai hukumar ta girka wani kwamiti mai mambobi 13 a karkashin jagorancin mataimakin shugaban hukumar wanda zai kara nazarin batun tare da tattaunawa da bangarori daban-daban musamman ma na siyasa domin jin shawarwarinsu kan batun jadawalin nan da kwanaki 15 masu zuwa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani