Kotun Ecowas ta tabbatar da nasarar Bazoum
May 31, 2022Kotun kungiyar kasashen Afrika ta yamma watau Ecowas ta yi watsi da karara da tsohon shugaban Jamhuriyyar Nijar Mahamane Osumane ya shigar inda ya kalubalanci zaben shugaban kasar da aka yi a bara, zaben da ya bai wa shugaba mai ci yanzu Mohammed Bazoum nasara. Tsohon shugaban ya yi zargin an tafka magudi da take hakkin jama’a, kotun ta bai wa Shugaba Bazoum nasara a shari’ar.
Korafe-korafe har guda takwas ne, dan takara a zaben shugaban kasa na jamhuriyyar Nijar karkashin jam'iyyar RDR Chanji Mohamane Ousman na jam'iyyar RDR Chanji ya gabatarwa kotun Ecowas din da ke Abuja, ta hannun lauyoyinsa karkashin jagoranci Maitre Lirwana Abdou-rahamane.
Daya bayan daya alkalin kotun Dupe Atoki da sauran alkalan suka yi watsi da korafe-korafe guda bawaki daga ciki, batun zargin aikata abubuwan da ba su dace ba a zaben, ta ce mai kara ya kasa bada shaidar tabbatara da haka, haka nan batun take hakkin jama’a na hana mutane taruwa ta ce, an yi ne don kaucewa afkuwar rikici.
Korafi daya ne na katse hanyar sadarwa ta internet inda kotun ta ce kodayake duk ta shafi bangarori biyu kuma an yi ne don katse masu aikawa da sakonni na tashin hankali, amma an take hakkin Mohamane Ousmane. Maitre Souley Dagouma na daga cikin lauyoyin da suka kare gwamnatin Jamhuriyyar Nijar a shari’ar.
‘’Wannan cire yanar gizo da akan yi don a kiyaye abubuwa da ba su da kyau, domin an fara kone-kone don ta haka ne ake kiran mutanen su fito, kotu ta ce wannan hujja da aka bada bai isa ba, domin gwamnati na da ‘yanci in taga abubuwan da ba su dace ba tana da ikon ta cire. Bisa wannan kotu ta ce bai isa ba, shi ne aka ce an take hakkinsa’’
Lauyan da ke kare Mohamane Ousmane dai ya ki cewa uffan bisa daliin, sai ya samu kwafin sakamakon shari’ar. Bisa ga abin da ya faru na sakamakon wannan shari’ar da aka dade ana tafkawa ko bangaren gwamnati na Shugaba Mohamed Bazoum za su ce sun sami cikakkiyara nasara a wannan shari’a kenan? Har ila yau ga Maitre Souley Dagouma.
‘’Mun yi nasara a kan wannan karar domin shari’a ce a kan harkara zabe, an yi shari’a iri iri, tun da muke ba mu taba ganin irin wannan shari’a ba, bayan an fadi shi ne aka sake kai ta kotun Cedeo, duka wadanan zarge-zarge kotu ta yi watsi da su’’
Sakamakon wannan shari’a ya nuna gwamnatin Nijar a karkashin Shugaba Mohamed Bazoum za ta samu kwanciyar hankali na ci gaba da mulkin kasar sanin cewa baya tunanin wata shari'a a kan sahihancin zabensa.