Beljiyam ta dakatar da macin rashin tsoro
March 26, 2016Talla
A yayin da yake bayani a wannan Asabar Ministan cikin gidan Beljiyam Jan Jambon ya nemi masu machin da su dageshi har zuwa nan da wasu makonni don kauce wa abin da zai je ya zo.
Ministan ya kara da cewar: "Har yanzu daukacin kasar na cikin wani yanayin barazanar tsaro. Muna ci gaba da neman muhimman bayanai yanzu haka,. Wannan ne kuma dalilin da ya sa muke kira ga 'yan kasar da kada su yi maci a gobe. Maimakon haka a dageshi zuwa wani lokaci."
A makon nan ne dai 'yan kasar Beljiyum suka shirya wani gangami domin nuna takaicinsu kan harin da Kungiyar IS ta kai a filin tashin jiragen sama da tashar karkashin kasa na Brussels inda mutane da dama suka mutu tare da jikata sama da dari daya.