Beljiyam ce ta uku a gasar Russia 2018
July 14, 2018Beljiyam ta lallasa Ingila da ci biyu da nema domin samun matsayi na uku a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.
Ana fara wannan wasa cikin mintoci hudu na farko dan wasan kasar Beljiyam mai suna Thomas Meunier ya jefa kwallo na farko a ragar Ingila.
Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Beljiyam ta samu wannan matsayi na uku, domin ta sha kashi a hannun Faransa a shekarar 1986 lokacin neman matsayin na uku a wasan da ya wakana a kasar Mexiko, wanda Argentina ta dauki kofi bayan doke Jamus a wasan karshe. Yayin da ita Ingila ta taba lashe kofin sau daya a shekarar 1966 lokacin da ta shirya gasar.
A gobe Lahadi ake kawo karshen gasar ta neman cin kofin kwallon kafa ta duniya, inda za a fafata tsakanin Faransa da Croatia a filin wasa na Luzhniki dake birnin Moscow.