1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benin: Gwajin Covid-19 a kan malaman makaranta

May 9, 2020

Hukumomi a kasar  Benin sun gudanar da wani gwajin coronavirus na musamman a kan malaman makaranta. Mahukumta sun dauki wannan mataki ne gabanin bude makarantu da suke shirin yi a ranar Litinin.

Der Präsident von Benin Patrice Talon
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Daga Litinin dai an amince daliban da ke ajin karshe a makarantun firamare har zuwa jami'o'i su koma makaranta. Matakin na zuwa ne bayan 'yan kasar sun yi akalla makonni shida a cikin dokar kulle wace ta tilasta rufe makarantu da sauran abubuwan rayuwa. Kawo yanzu kasar Benin mai mutane milyan 11 na da masu coronavirus guda 284, a cikin adadin kuma mutum biyu sun rigamu gidan gaskiya.