Isra'ila: Tuhuma kan Benjamin Netanyahu
October 2, 2019Talla
Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan zaben da har yanzu bai kammalu ba a Isra'ilan, sakamakon rashin samun cikakkiyar nasara ga duka 'yan takarar da za ta ba su damar kafa gwamnati. Zaben wanda aka gudanar da shi har sau biyu cikin shekara guda ba tare da samun nasarar kafa gwamnatin ba, ya sanya Firaminista Benjamin Netanyahu da ke zaman dan jam'iyya mai mulki ta Likud fafutukar ganin ya samu nasarar kafa gawamnatin hadaka domin kara tsawon wa'adin mulkinsa. Abokin hamayyarsa da suke tafiya kai da kai a wannan zabe da shi na jam'iyyar Blue and White Benny Gantz dai ya ki amincewa da hada kai da Natanyahu domin kafa gwamnatin hadakar, sakamakon zarge-zargen da ake wa Natanyahun dangane da cin hanci da rashin gaskiya da kuma zamba.