Benny Gantz ya bijire wa Netanyahu
September 19, 2019Talla
Duk da cewa Benny Gantz din da Benjamin Netanyahu sun amince da batun kafa gwamnati amma sun kasa samu matsaya a kan wa zai jagoranci tafiyar.
Moshe Yaalon wani kusa a jamiyyar ta Gantz ya tabatar da ba zasu shiga gwamnatin hadin gwiwa da Firai minista Netanyahu zai jagoranta ba, wanda hakan ya sa tsohon hafsan sojin Ganz ya baiyana aniyar shi ta jagorantar tafiyar.
Tuni dai Firai Minista Netanyahu yai Allah wadai da wannan mataki na Gantz da ma jamiyyar tasa suka dauka, a wani sakon bidiyo da ya fitar, ya ce ya yi matukar mamaki da ma takaicin wannan shawara ta Gantz. Ya kara da cewa kofa a bude take don tataunawa.
Wannan dai shi ne zaben da kasar ta yi a karo na biyu a wannan shekarar.