1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benzema zai kai Faransa kotu

Abdul-raheem Hassan
October 19, 2023

Lauyan dan wasan kwallon kafa Karim Benzema, ya sha alwashin kalubalantar ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Faransa a gaban kotu kan zarginsa da alaka da kungiyar Hamas ta Faladsinu.

Dan wasan kungiyar kungiyar Al-Itihad a a Saudiyya Karim BenzemaHoto: AP/dpa/picture alliance

Ministan cikin gida a kasar Faransa Gerald Darmanin ya yi wannan zargin ne bayan da Benzema da ke taka leda a kungiyar Al-Itihad ta Saudiyya ya wallafa wani sako a shafukan sada zumunta game da rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Faladsinu, inda dan wasan yake cewa "Dukkan addu'o'inmu ga mazauna Gaza ne wadanda suka sake fuskantar wadannan hare-haren bama-bamai na rashin adalci wadanda ba su bar mata ko yara ba," sakon da Benzema ya wallafa a shafin X, wanda a baya aka fi sani da Twitter."

Da yake magana a gidan talabijin na CNews, ministan cikin gida na Faransa Darmanin ya zargi Benzema da cewa "Yana da mummunar alaka da kungiyar 'yan uwa musulmi", kungiyar 'yan Sunni musulmi da ta samo asali daga kasar Masar wanda a halin yanzu gwamnatin Alkahira ta haramta.

"Wannan karya ce! Karim Benzema bai taba samun 'yar dangantaka da wannan kungiya ba," in ji lauyan da ke kare dan wasan Layer Benzema Hugues Vigier a cikin wata sanarwa. Lauyan ya cigaba da cewa Benzema yana nuna "tausayi na dabi'a" tare da "abin da mutane da yawa a yau suke kwatanta da laifukan yaki da ake aikatawa a Gaza, amma wanda bai kawar da ta'addancin 7 ga watan Oktoba ba, wani abu da ba za a tattauna ba".

Lauyan ya kara da cewa yana shirin shigar da kara a kan Darmanin kan kalaman nasa. Benzema, mai shekaru 35, wanda aka haifa a Faransa iyayensa 'yan asalin kasar Aljeriya, ya kasance daya daga cikin fitattun taurarin da ke taka wa Faransa leda a cikin shekaru 10 da suka gabata.