1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Berlin: Gidauniyar farfado da Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
June 11, 2024

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sake gabatar da bukatar neman taimakon makaman kariyar sararin samaniya da kuma kudade domin sake gina tashar makamashin wutar lantarki ta kasar da yaki ya daidaita.

Berlin | Scholz da Selenskyj gidauniya raya Ukraine
Berlin | Scholz da Selenskyj gidauniya raya UkraineHoto: Britta Pedersen/dpa/picture alliance

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sake gabatar da bukatar neman taimakon jiragen yaki da makaman kariyar sararin samaniya da kuma kudade domin sake gina tashar makamashin wutar lantarki ta kasar da yaki ya daidaita. Ya gabatar da rokon ne a jawabinsa a taron sake farfado da Ukraine da ya gudana a birnin Berlin a Jamus.

Zelensky ya ce kasarsa na bukatar akalla manyan makamai masu linzami samfurin Patriot guda bakwai cikin takaitaccen lokaci domin kare manyan biranen kasar daga yawan luguden wutar da Rasha ke yi musu ta sama.

Ya ce wadannan hare hare na Rasha sun mayar da hankali ne musamman akan cibiyoyin wutar lantarki da kuma sauran wurare inda suke yin mummunan ta'adi.

Ya kuma gode wa gwamnatin Jamus wadda ta dauki nauyin taron bisa kokarinta na taimaka wa Ukraine da makaman kariyar sararin samaniya samfurin Patriot guda biyu da kuma wasu tallafin tare da alkawarin karin tallafin kashi na uku.