1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Joe Biden zai gana Xi Jinpin

Abdourahamane Hassane
November 10, 2022

Shugaban kasar Amirka Joe Biden zai gana da takwaransa na china Xi Jinping a birnin Bali na kasar Indonesiya a dabra da taron kasashe masu arzikin masantu G20.

USA | Joe Biden im virtuellen Gespräch mit Xi Jinping
Hoto: Susan Walsh/AP/picture alliance

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake yin takun saka tsakanin manyan kasashen duniyar guda biyu. Shugabannin biyu, wadanda za su yi ganawa ta farko ta  ido da ido tun bayan zaben Joe Biden, za su tattauna kan yadda za a kawar da goggayar da ke a tsakanin kasahen biyu domin yin aiki tare. Biden da Xi Jinping, wadanda suka riga suka yi magana sau da yawa ta wayar tarho  tare da yin taron bidiyo. Za su kuma tattauna jerin batutuwan kasa da kasa a ciki har a na Taiwan wanda shi ne tushen rikici tsakanin China da Amirka bayan ziyarar da kakakin majalisar dokokin Amirkan ta kai a Taiwan