SiyasaArewacin Amurka
Biden ya bukaci kawo karshen yakin Sudan cikin hanzari
September 18, 2024Talla
A wata sanarwa da shugaban ya fitar, ya ce yakin na Sudan ya dagula al'amuran shigar da kayan agajin jin kai da kuma ke kasancewa mafi muni a al'amuran da suka shafi agajin gaggawa a duniya. Kazalika yakin ya jefe rayuwar mata da kananan yara cikin tsaka mai wuya da ke fuskantar barazanar 'yunwa da fyade kusan a kowacce rana.
Karin bayani: RSF ta halaka fararen hula da dama a Sudan
Biden ya bukaci warware takaddamar da ke tsakanin shugaban rundunar sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa kuma shugaban rundunar kar-ta-kwana ta RSF Mohamed Hamdan Daglo da suka raba gari tun a watan Afrilun shekara ta 2023.