1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Biden ya ce sake mamayar Gaza babban kuskure ne

October 16, 2023

A daidai lokacin da dakararun Isra'ila ke shirin kai farmaki ta kasa kan Kungiyar Hamas a zirin Gaza, Shugaban Amirka Joe Biden ya bayyana yunkuri da Isra'ilar ke yi na sake mamayar zirin a matsayin babban kuskure.

Shugaba Biden ya bayyana sake mamayar Gaza a matsayin babban kuskureHoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

Shugaba Joe Biden ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wani gidan talabijin inda ya kara da cewa Hamas ba ta wakiltar dukkan al'ummar Faladsinu amma kuma kawar da masu tsatsauran ra'ayi matakin ne mai kyau.

Karin bayani: Isra'ila za ta shiga sabon babi na yaki a Zirin Gaza

Shugaban na Amurka ya kuma ce ba ya ganin decewar sojojin Amurka su shiga wannan rikici, kuma ba za a tura su Ukraine ba domin shigar wa Kiev fadan da take yi da Rasha.

Biden ya karkare yana mai cewa Isra'ila na da sojoji masu cikekken horo kuma Amurka za ta ba su goyon baya. Tuni ma dai gwamnatin Washington ta sanar da sake tura jirgin ruwan yaki  i zuwa Gabashin Tekun Bahar Rum, wanda ke zama jirgi na biyu da ta tura tun bayan barkewar rikicin Hamas da Isra'ila a ranar Asabar (08.10.2023). 

Karin bayani:Jamus ta fara aikin kwashe 'ya'yanta daga Isra'ila