Biden ya gana da ministocin Ukraine
March 26, 2022Wannan dai na kasancewa karon farko da shugaba Biden ya gana da manyan jami'an Kyiv gaba-da-gaba tun bayan da Rasha ta fara mamaya a Ukraine. Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba da takwaransa na tsaro Oleksii Reznikov na fatan samun karin kwarin gwiwar yaki a wannan ganawar.
Kuleba ya ce sun tattauna kan sabbin takunkuman da za a kakabawa Rasha da kuma yadda za ta dandana kudarta idan aka aiwatar da su yadda suka kamata.
An dai gudanar da tattaunawar ce tsakanin bangarorin biyu a kusa da filin jirgin kasa na birnin Warsaw, inda a nan ne ake samun kwararar 'yan gudun hijira da ke tserewa yakin Ukraine. Yayin da yake ganawa da 'yan gudun hijrarar, shugaba Biden ya baiyana shugaba Vladmir Putin na Rashar a matsayin "dan ina da kisa" ya na mai nuna rashin gamsuwa da ikrarin da Rasha ta yi na rage manufofin ci gaba da yaki.