Biden ya ki danganta Rasha da ta'addanci
September 7, 2022Amirka ta ce ba ta da niyyar ayyana Rasha a matsayin kasar da ke dauyin ta'addanci. Shugaban majalisar tsaro ta Amirka John Kirby ya ce yin hakan ba shi ne mataki mafi dacewa na ganin Rasha ta girbi abin da ta shuka ba.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ne dai ya yi kira ga kasashen yamma su ayyana Rasha a hukumance a matsayin kasar da ke daukar nauyin ta'addanci sakamakon hare haren da suka hallaka fararen hula musamman a wani kantin sayar da kaya da ke Kremenchuk a watan Juni inda akalla mutane 18 suka rasu.
A waje guda hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci samar da tsaro da kariya a kusa da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia wadda Rasha ta mamaye yayin da ake cigaba da luguden wuta a yankin.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Rasha da Ukraine su samar da wata da'ira da za a daina fada kusa da tashar makamashin nukiliyar ta Zaporizhia