1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Biden ya yi alkawarin mika wa Trump mulki cikin ruwan sanhi

November 7, 2024

Shugaba Joe Biden ya gayyaci Donald Trump da ya zo su shirya yadda za a mika wa sabuwar gwamnatin ragamar mulki, sa'o'i kadan bayan nasarar jam'iyyar Republican a zaben shugaban kasar Amurka.

Biden zai mika wa Trump mulki cikin ruwan sanhi
Biden zai mika wa Trump mulki cikin ruwan sanhiHoto: Douliery Olivier/abaca/picture alliance

Shugaba Joe Biden ya yi alkawari a wannan Alhamis na mika mulki cikin ruwan sanyi ga sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump wanda ya lashe zaben kasar na ranar biyar ga wannan wata na Nuwamba.

Karin bayani: Shugabannin duniya na taya Trump murnar lashe zabe

A yayin wani jawabi da ya gabatar daga fadar mulki ta White House, shugaban mai barin gado ya ce akwai bukatar kawo karshen dambarwar siyasa da Amurka ke fuskanta musamman tsakanin magoya bayan jam'iyyar Demokrat da na Republican.

Tuni ma dai Shugaba Biden ya gayyaci Trump da ya zo su shirya yadda za a mika wa sabuwar gwamnatin ragamar mulki, sai dai bai tsayar da ranar gayyatar ba.

Ana dai sa ran manyan mutane da dama za su taka rawa a sabuwar gwamnatin da shugaba mai jiran gado Trump zai kafa, ciki har da hamshakin dan kasuwar nan Elon Musk wanda ya mallaki kamfanin X da kuma kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki na Tesla.