1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya zargi Putin da aikata laifukan yaki

April 4, 2022

Shugaba Joe Biden na kasar Amirka ya zargi shugaba Vladmir Putin na Rasha da aikata laifukan yaki tare da neman a gurfanar da shugaban na Rasha.

USA Washington | Joe Biden
Hoto: Patrick Semansky/AP/picture alliance

Hakan dai na zuwa ne a yayin da duniya ke ci gaba da yin tir da kisan kiyashin da ake zargin Rasha da aikatawa a Bucha da ke kusa da birnin Kyiv na Ukraine.

Shugaba Biden ya ce hotunan sun nuna karar irin ta'asar da Putin din ya yi a Ukraine wanda suka nuna hujojjin gurfanar da shi a gaban kotun hukunta laifukan yaki. Shugaban na Amirka ya ce za su cigaba da bai wa Ukraine tallafin kayayyakin yaki da zai ba ta damar ci gaba da yaki.