1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BIKIN CIKA SHEKARU 60 DA KAWO KARSHEN YAKIN DUNIYA NA BIYU.

YAHAYA AHMEDMay 9, 2005

An dade ba a son tunawa da ran 8 ga watan Mayu a nan Jamus. Saboda rana ce da ke alamta kawo karshen yakin duniya na biyu da kuma kayen da Jamus ta sha a wannan yakin. Sai lokacin shugaban kasa Richard von Weizsäcker ne, aka sami wani sauyi na kallon da ake yi wa wannan ranar a nan kasar, yayin da ya yi jawabi ga taron majalisar dokoki ta Bundestag a cikin shekarar 1985. A bukuwan da ake yi na cika shekaru 60 da kawo karshen yakin duniya na biyun, kafofin yada labarai da yawa a nan Jamus, sun yi ta sharhohi daban-daban kan muhimmancin wannan ranar, ga duniya, da nahiyar Turai, da kuma ga Jamus, kasar da ta janyo barkewar yakin.

Shugaban kasa Horst Köhler da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Gerhard Schröder, a bikin dora furanni don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a yakin duniya na biyu, da aka yi a Berlin a ran 8 ga watan Mayu.
Shugaban kasa Horst Köhler da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Gerhard Schröder, a bikin dora furanni don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a yakin duniya na biyu, da aka yi a Berlin a ran 8 ga watan Mayu.Hoto: AP

A cikin jawabinsa na bukuwan tunawa da cika shekaru 60 da kawo karshen yakin duniya na biyu a nan Jamus, shugaban majalisar dokokin tarayya ta Bundestag, Wolfgang Thierse, ya bayyana cewa, tsayawa daran dakau, wajen yin nazari kan danyen aikin da Jamus ta gudanar a lokacin yakin na biyu, ya zamo ruwan dare ga duk Jamusawa. Wannan shadarar dai ta zo daidai da jigon jawabin da shugaban kasa Horst Köhler ya yi game da bikin: wato Jamus a yau, ta bambanta da Jamus din da aka sani a shekaru 60 da suka wuce.

Dukkansu dai na da gaskiya. Yau a nan Jamus, babu wata muhawarar da ake yi kuma, kan ko ranar 8 ga watan Mayu, rana ce ta shan kaye, ko kuma rana ce ta `yantad da Turai daga hannun `yan mulkin kama karya na gwamnatin Nazi. Kusan kashi 80 cikin dari na al’umman Jamus ne ke goyon bayan ra’ayin da tsohon shugaban kasa, Richard von Weizsäcker, ya bayyanar a cikin jawabinsa, shekaru 20 da suka wuce.

Kazalika kuma, a yau, babu wanda ke musanta cewa, duk gallaza wa Jamusawa da aka yi a lokacin yakin duniya na biyun da kuma abin da ya biyo bayansa, kamar korar kusan Jamusawa miliyan 12 da aka yi a gabashin Turai, suna da asalinsu ne daga akida da kuma manufofin da Adolf Hitler ya gabatar kuma yake bi. Sabili da haka ne kuwa, wasu masana tarihi ke ganin cewa, wargajewar Jamus ta fara ne a ran 30 ga watan Janairu na 1933, ran da Adolf Hitlern ya hau karagar mulki, amma ba a loakcin yakin duniya na biyun ba. Kamar dai yadda shugaban kasa Horst Köhler ya bayyanar, wannan sashe na tarihin Jamus, ba abu ne da za a taba iya mantawa ko kuma yin watsi da shi ba. Ko yaushe, ya kamata, a yi ta tunasad da jama’a kan irin duk ayyukan assha da suka auku a lokacin yakin da kuma irin mulkin kama karyar da gwamnatin Nazi ta yi, don kada a sake samun maimaitawar hakan a nan Jamus.

Duk dai wadannan ra’ayoyin na samun amincewar mafi yawan Jamusawa. Kuma hakan ne ya share fagen bai wa mahukuntan Jamus karfin gwiwa, wajen daukar matsayin hannunka mai sanda a bukukuwan cika shekaru 60 da kawo karshen wannan mummunan yakin. Shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder, ya dau muhimman matakai a wannan huskar. Ban da dai kasancewarsa, farkon shugaban gwamnatin Jamus da aka taba gayyata ya halarci bikin tunawa da kawo karshen yakin a birnin Moscow, Gerhard Schröder, a cikin wata makalarsa da aka buga a jaridar nan ta „Komsomolskaja Prawda“ ta kasara Rsaha, ya kuma nemi gafara a madadin duk Jamusawa, daga al’umman Rashan, game irin azabar da aka nuna musu da sunan Jamus, a lokacin yakin duniya na biyun.

Shugaban kasa Hosrt Köhler ma ya bi wannan misalin, yayin da ya sadu da wadanda suka tsira daga danyayan aikin da aka gudanar a lokacin yakin duniya na biyun da kuma bayansa, wadanda har ila yau ke nan da ransu, a nan Jamus. A daura da wani shugaban kasar da aka taba samu a nan Jamus dai, Horst Köhler bai yi wata-wata ba, wajen yin ambato dalla-dalla na irin azabar da Jamusawa ma suka huskanta a shekarar 1945 da kuma bayan haka, kamar dai su fyade da ya wuce gona da iri, da tura jamusawa da yawa zuwa aikin dole a sansanonin Rasha, da mutuwar da wasu da dama suka yi, da korar da aka yi wa Jamusawa mliliyan 12 daga gabashin Turai, inda kusan milian 2 ne suka rasa rayukansu. Babu shakka, tunawa da Jamusawan da su ma aka gallaza musu a loakcin wannan yakin yana da muhimmanci ainun.

A wannan huskar dai, jama’ar birnin Berlin da suka ga karshen yakin duniya na biyun ne batun ya fi shafa. Babu dai wadanda suka fi ganin masifa a biranen Jamus, kamar al’umman wannan birnin, a ranakun karshen yakin. Sabili da haka ne kuwa, suka fito a dubbaninsu a ran 8 ga watan Mayu, don halartar bikin da majalisar dattijan birnin ta shirya a gaban dandalin nan da ke kofar Brandenburg, wanda ta yi wa suna “bikin dimukradiyya”. An dai tsananta matakan tsaro, don hana ta da zaune tsaye da mabiya sabon salo na akidar Nazin suka yi niyyar yi. Ga mazauna birnin Berlin dai, haramta taron `yan tsagerun da aka yi, ita ce babbar nasarar da dimukradiyya ta samu a wannan ranar ta 8. ga watan Mayu.