Bikin cikwan shekaru 50 da girka EU
March 24, 2007Ƙasashe 6 ne da tashin farko su ka haɗu domin girka tubalin tushen ƙungiyar gamaya turai,wadda yau, ta zama babbar mattatara ta ƙashe 27.
Ranar 25 ga watan Maris na shekara ta 1957,Ƙasashen France, Italia, Jamus, Belgium Luxemburg, da kuma Holland su ka haɗu domin girka wannan ƙungiya, da ta kasance yau tarmamauwa sha kallo, a fagen diplomatia na dunia.
Domin ƙaddamar da bukukuwan cikwan shekaru 50 shugabanin ƙasshen EU, sun hallara tun ranar jiya a birnin Berlin nan Jamus bisa jagorancin shugabar gwamnmati Angeller Merkell,wadda a halin yanzu ke jagorantar ƙungiyar EU.
A wannan haɗuwa, shugabanin sun yi waiwaye addon tafiya a game da nasarori da kuma matsalolin da EU ta cimma , kazalika nan gaba a yau za su bayana sanarwar hadin gwiwa wadda ta ƙunshi sabin matakai da su ka tanada domin inganta wannan ƙungiya.
Wasu daga mahimman nasarorin da EU ta cimma a tsawan wannan lokaci, sun haɗa da girka kuɗin Euro na bai ɗaya da kuma ƙungiyoyi daban--daban na cuɗe ni in cuɗe ka ta fannin tatatalin arziki da kyauatta rayuwar al´ummmomi fiye da milion 300, na ƙashe membobin EU.
Wasu daga wannan matakai sun haɗa da yarjejniyar Schengen wadda ta tanadi walwala ta fannin zirga zirga a ƙasashen EU tsakanin al´ummmmoin su.
Kazalika, ƙasashen na magana tsintsiya maɗaurin ki ɗaya a dandalin siyasa da na diplomatia a dunia, ta hanyar komishinoni daban-daban da kuma majalisar taraya.
Saidai duk da wannan nasarori ƙungiyar taraya turai, na fuskantar manyan ƙalubale, mussaman ta la´akari da har yanzu, sun ka kasa cimma girka kundin tsarin mulki da kuma rundunar tarrayya.
Shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkel a jawabin da ta gudanar, a taron ta bayana wasu mahimman kalubalen da EU zata fuskanta a shekaru masu zuwa:
„Ya zama wajibi, mu ƙara kaifin harakokin mu na diplomatia, sannan baki ɗaya mu tashi tasyin daka, domin yaƙi da ta´danci, da kuma ƙara samun husa´ao´in fuskantar ƙalubale a wannan dunia.
Wani babban burin kuma shine mu sake hauda taraya turai a kann sabuwar ingantar turba ta tsarin mulki, kamin nanda zabbukan yan majalisu taraya a shekara ta 2009“.
A wani fannin kuma shugabar gwamnatin Jamus, ta bada shawara girka rundunar haɗin gwiwa tsakanin dukan ƙasashe membobin EU.