Habasha: Bikin maido da kayayyakin tarihi
November 20, 2021Talla
A wannan Asabar aka baje kayayyakin a kofar wani ginin ajiyan kayayyakin tarihin kasar don kowa ya gani. Jakadan kasar a Britaniya Teferi Melesse, da aka mika wa kayayyakin a hukumance watanni biyu da suka gabata a Britaniyan kafin ya kai su Addis Ababa, ya baiyana farin cikinsa inda ya baiyana nasarar maido da kayayyakin a matsayin gagarumin ci gaba mai matukar tasiri.
Habasha ta bi sahun sauran kasashen Afirka, da ke ci gaba da yin kira ga kasashen da suka sace kayayyakin tarihinsu a lokacin mulkin mallaka da su gaggauta maido su a maimakon adon da suke yi da su a dakunan tarihinsu a kasashen nahiyar Turai.