1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Bikin "ranar" Hausa

August 26, 2025

An gudanar da bikin ranar Hausa ta duniya ta kowacce ranar 26 ga watan Agusta domin yin bikin ranar kuma an gudanar da bikin wannan shekarar a garin Daura da ke jihar katsina a Najeriya.

Ganga
GangaHoto: Faruq Azam/DW

 

An yi a fadar maimartaba Sarkin Daura da ake wa lakabi da tushen Hausa an gudanar da nuna al'adun Hausa iri-iri domin kayata kuma taken bikin na bana shi ne amfani da harshen Hausa wajen wanzar da zaman lafiya. Abdulbaki Jari na daga cikin wadanda suke shirya bikin Kuma shi ne ya assasa bikin wannan rana ta kokarin ganin Majalisar Dunkin Duniya ta amince da ita.

Karin Bayani: Cece-kuce kan amfani da harshen Hausa a Jamhuriyar Nijar

Mahalarta taron sun yi Imani da cewa taron zai kara hada kan Hausawa a duk inda suke a cewar Kanal Muhammad Sani Masallaci Gwamnan jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar wanda ya jagoranci tawagar kasar ta Nijar zuwa taron harshen Hausa na daga cikin abin da ya kara kula alakar kasashen biyu.

Hira da Sarkin Hausawa na Agege da ke Lagos

03:23

This browser does not support the video element.

Duk da daukar shekaru goma ana wannan bikin na ranar Hausa har yanzu harshen na fuskantar kalubale abin da Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida ke cewa akwai bukatar gudummuwar kowa da kowa. Makadan Hausa da mawaka da 'yan kokowa da wanzamai da makera duk sun bake kolin al'adunsu a wannan rana inda suka nishadantar da mahalarta taron.