1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar masu bukata ta musamman a Njiar

July 31, 2018

Masu bukata ta musamman a Nijar sun wayar da kai a yankunan kasar game da fa'idojin ilimi da kiwon lafiyar mata da yara kanana albarkacin ranarsu.

Behinderte in Arika - Rollstuhlfahrer
Hoto: picture-alliance/dpa

A Jamhuriyar Nijar tun bayan da gwamnatin kasar ta sa hannu kan yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya game da batun kare hakkin nakasassu a shekarar 2008, hukumomin kasar suka  ware kowace ranar 31 ga watan Yuli a zaman ranar nakasassu. A bana, jihar Damagaram ce aka zaba domin gudanar babban bikin na kasa. Sai dai nakasassun sun zargi ministan al’umma da yi wa lamarin rikon sakainar kasha.

Nijar dai na da nakasassu dubu 700 da duriya ne, wato kwatankwacin kashi 4.1 % na yawan al’umar  kasa kuma galibinsu matasa ne masu jini a jika. Nakasassun sun gudanar da rangadin wayar da kai a yankunan Dosso da Tahoua da Maradi da kuma Damagaram, rangadin da ke a matakin farko na wayar da kan nakasassu game da muhimmancin ilimi da kuma kiwon lafiyar mata da yara kanana.

A karshe kungiyar nakasassun ta kasa ta ce har yanzu da sauran rina a kaba wajen nuna masu wariya ta musaman a irin wannan rana, kamar yadda Bunu Issa shugaban kungiyar a Damagaram ya shaida wa tashar DW.