1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNijar

Jamhuriyar Nijar: Bikin ranar 'yancin mata

Gazali Abdou Tasawa LMJ
May 13, 2025

A ranar 13 ga watan Mayu na kowacce shekara, ake bikin 'yancin mata ta Jamhuriyar Nijar da aka kaddamar shekaru 33 da suka gabata.

Jamhuriyar Nijar | Mata | Ranar Mata
Duk da matsalar tsaro, mata na fita domin kada kuri'unsu a lokutan zabeHoto: Marou Issa Madougou/DW

An dai kaddamar da wannan rana ta 'yancin mata a Jamhuriyar Nijar, domin tunawa da wata kasaitacciyar zanga-zanga da matan kasar suka gudanar da nufin neman a kara musu yawan kujerun wakilci a babban taron muhawara na kasa wato Conference Nationale wanda ya kai ga maida kasar kan turbar dimukuradiyya. Albarkacin wannan rana, kowace shekara matan kasar ta Nijar kan shirya taruka dabam-dabam na yin bitar irin ci-gaba ko akasinsa da mata suka samu a fannin 'yancinsu.  Kungiyoyin matan Nijar sun gudanar da taruka dabam-dabam, inda aka kaddamar da wani titi na musmaman a birnin Yamai da nufin karrama matan kasar. A hannu guda kuma, wasu kungiyoyin matan sun kai gudunmawa ga 'yan uwansu mata a wasu kauyukan jihar Tillabery da ta'addanci suka daidaita. A jawabin da ta gabatar albarkacin wannan rana, ministar al'umma Farfesa Sadikou Ramatou Djermakoy ta jinjinawa matan kasar ta Nijar dangane da gwagwarmayar da suke yi wajen samar da 'yancin nasu da ma na kasa baki daya. To amma wasu ma na ganin 'yancin matan ya fuskanci koma-baya a shekarun baya-bayan nan, a Jamhuriyar ta Nijar.