1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin rantsar da sabon shugaba Jonathan na Nijeriya

Umaru AliyuMay 29, 2011

Ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu, aka yi bikin rantsar sabon shugaban kasa na taraiyar Najeriya, Goodluck Jonathan, sakamakon nasarar da ya samu lokacin zaben shugaban kasa a watan Aprilu

Goodluck Jonathan sabon shugaban NajeriyaHoto: AP

Ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu, aka yi bikin rantsar sabon shugaban kasa na taraiyar Najeriya, Goodluck Jonathan. Bikin an gudanar dashi ne a dandalin da ake kira Eagle Squire a birnin Abuja, karkashin jagorancin babban jojin kasar, Alkali Alysius Katsina-Alu, gaban dimbin yan kallo da manyan baki da shugabanni daga ko ina cikin Afirka. Lokacin rantsar dashi, shugaba Jonathan yayi alkawarin biyayya ga tsarin mulki da dukkanin yan Najeriya, kuma yace zai tafiyar da aiki da nauyin da aka dora kansa cikin gaskiya da rikon amana iyakacin karfin sa.

Sabon shugaban na Najeriya, wannan shine karo na farko da aka rantsar dashi a matsayin zabben shugaban kasa, sakamakon kuri'un da aka kada a watan Aprilu. Kafin wannan lokaci Jonathan yayi shekara guda yana cike wa'adin mulkin marigayi shugaban kasa, Umaru Musa Yar Adua, wanda ya rasu kafin wa'adin mulkin sa ya cika. Sabon shugaban shine kuma na farko daga jerin tsirarun kabilu da suka fito daga yankin Niger Delta dake fama da fadi-tashi a yanzu.

Sai dai kuma masana sun baiyana cewar shugaban. dan shekaru 53 da haihuwa, ya karbi mulkie a daidai lokacin da Najeriya take fama da karkasuwa, musmaman a sakamakon zabubbukan da aka yi a watan Aprilu. Saboda haka ne daga cikin matakan da zai dauka har da bunkasa tsaro da neman kyautata jin dadin zaman jama'a, ciki kuwa har da rage matsalar karancin man fetur da karfin lantarki da hadin kai tsakanin kabilun kasar.

Bayan shugaban kasa, an kuma yi gudanar da bukukuwan rantsar da gwamnonin jihohin kasar ta Nijeriya. Muna dauke da rahoto daga wakilin mu na Abuja, Ubale Musa kan yadda bikin ya gudana a can da kuma wakilin mu na Kano, Babangida Jibril, game da bikin rantsar da gwamnan jihar sai kuma yankin Niger Delta inda wakilin mu, Muhammad Bello ya shaida mana yadda aka gudanard a bukukuwa a jihohin wannan yanki.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Abdullahi Tanko Bala