Bikin tunawa da hatsarin tashar nukiliya ta Fukushima a Japan
March 11, 2013Talla
Hukumomi da al'umma a ƙasar Japan sun yi tsit na wasu 'yan mintoci, domin tunawa da hatsarin nukiliyar na tashar Fukushima da aka samu, a sakamakon girgizar ƙasar da ta haddasa igiyar ruwa ta tsunami, da suka afkawa yankin arewa maso gabashi na ƙasar a cikin watan Maris na shekara ta 2011.
An gudanar da bukukuwa na tunawa da hatsarin a garuruwan Tokyo da kuma inda lamarin ya auku, tare da halarta shugabanni da kuma sarakunan gargajiya.. Dubun dubatar masu zanga zangar ƙin jinin nukiliya sun gudanar da wani gangami a cikin ƙasashe daban daban na duniya. A yanzu dai tashoshin nukiliyar guda biyu ne suke aiki, bayan an rufe sauran tashoshin sakamakon girgizar kasar.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal