1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin tunawa da Mandela a Ghana

July 18, 2017

A birnin Accra na kasar Ghana an yi bikin tunawa da ranar haihuwar Nelson Mandela inda aka gudanar da wasu ayyuka na inganta rayuwar al’ummar yankin Nima mai fama da tarin matsaloli.

Trauer Mandela Südafrika
Hoto: Reuters

Ranar 18 ga watan Yuli rana ce da ofishin Majalisar Dinkin Duniya ta ware don gudanar da bikin tunawa da ranar haihuwar  tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela, sai dai bikin na bana ya dauki sabon salo ganin yadda majalisar ta yi anfani da ranar don janyo hankulan masu ruwa da tsaki a kokarin kawar da talauci da ya addabi al’ummar nahiyar.

An dauki tsawon sa’oi 67 daidai da shekarun da Mandela ya kwashe yana aikin raya kasa don tsaftace wasu yankunan da ake da matsaloli na rashin tsafta da talauci a wannan rana, an kuma soma wannan aikin na gama gari daga wata makaranta mai suna Nima Cluster of Schools don karrama Mandela a wannan lokaci da ake bikin zagayowar ranar haihuwar sa, yaki da talauci ko Action against Poverty shi ne taken bikin na bana kamar yadda Majalisar ta shirya a wannan rana ta tunawa da gwarzon Afrika kuma tsohon shugaban na Afrika ta Kudu Nelson Madiba Mandela. Marigayi Nelson Mandela ya kasance tauraro a Nahiyar Afirka dama duniya ba ki daya, a lokacin da ya ke raye ya yi iya kokarin magance matsalar matsanancin yunwa da talauci da ya addabi al'ummar nahiyar inda har ya zuba dukiyarsa wurin ciyar da marayu da ke rayuwa a gidajen da aka tanadar musu akalla 50.

Hoto: ISNA

Daya daga cikin abinda za’a iya cewa ya fi daukar hankali a bikin na bana shi ne,yadda aka  gudanar da wannan kasaitaccen biki a wani  yankin birnin na Accra mai suna Nima da ke fama da tarin matsaloli kama daga cunkoson jama’a da rashin tsafta da karancin asibitoci dama makarantu. 

A karshe dai daliban makarantar Nima 2 cluster da suka ci gajiyar bikin na bana sun bayyana farin cikin su ganin nan ba da dadewa ba za a kammala ginin makarantar Sakanadaren da aka shirya sa wa suna Mandela Block don karrama tsohon shugaban na Afrika ta Kudu da ya rasu a shekarar 2013 yana da shekaru 95 a duniya.