A birnin Moscow na kasar Rasha an gudanar da faretin sojoji domin murnar cika shekaru 78 da nasarar da Tarayyar Soviet ta samu a kan sojojin Nazi na Jamus, a lokacin yakin duniya na biyu tsakanin 1941 zuwa 1945.
Talla
Ana dai gudanar da wannan bikin a ranakun tara ga watan Mayu na kowace shekara, kuma faretin na bana a cewar ma'aikatar tsaron Rasha ya kunshi sojoji dubu 10 da suka hadar da sojoji 530 da ke fafata yaki a Ukraine. A yayin faretin tunawa da nasarar da aka yi a kan sojojin NAZI da aka gudanar a dandalin Red Square a birnin Veliky Vovgorod na Rashan, an baje kolin tankokin yaki samfurin T-34 da motar yaki samfurin komai da ruwanka Tiger da makaman kakkabo jiragen sama S-400 da makamai masu linzami samfurin Yars da kuma motoci da ke dauke da makamai masu guba. Sojoji 1,000 da suka yi shiga ta kayan sarki na zamanin yakin duniya na biyu, sun rika yi maci suna wucewa gaban shugaban kasar da manyan baki.
Sai dai ba kamar shekarun baya ba, a bana an takaita bikin sannan babu shawagin jiragen yaki. Tsohon shugaban kasar Tarayyar Soviet Josef Stalin shi ne ya fara bayar da umarnin gudanar da bikin a watan Yunin 1945, inda shugaban Rasha da aka zaba ta dimukuradiyya Boris Yeltsin a 1995 ya mayar da ranar murnar nasarar da suka samu a kan sojojin Nazi na Jamus ta zama biki da za a rika yi duk shekara. A karkashin Shugaba Vladmir Putin kuma, aka mayar da ranar ta nuna karfin tasiri na makaman soji. Sai dai an soke bikin faretin a wasu garuruwa da biranen Rasha da ke iyaka da kasar Ukraine, saboda matsaloli na tsaro.
Shekara guda da fara yakin Rasha da Ukraine
A ranar 24 ga watan Fabarairun 2022, al'ummar Ukraine suka wayi gari da tashin bama-bamai daga kasar Rasha.
Hoto: Bulent Kilic/AFP
Bakar rana ga miliyoyin al'ummar Ukraine
A ranar 24 ga watan Fabarairun 2022, al'ummar Ukraine suka wayi gari da tashin bama-bamai. Sojojin Rasha sun mamaye kan iyakokinsu da Rashan da ma Belarus da kuma yankunan da Rashan ta mayar da su karkashin ikonta tun shekara ta 2014. An kai hari a Ukraine, tuni aka fara hadawa da hukumomin gwamnati da kuma ya fara shafar al'umma.
Hoto: Ukrainian President s Office/Zuma/imago images
Hare-haren rashin imani
Shugaba Vladmir Putin na Rasha, ya bayyana harin da "matakin soja na musamman". Yana son karbe iko da yankunan Donezk da Luhansk. Mazauna birnin Mariupol, sun kwashe mako guda a ginin karkashin kasa na gidajensu. Da dama sun mutu a karkashin gine-ginen da suka rushe, kamar wasu daruruwa da suka mutu a karkashin baraguzan ginin wani gidan kallo.
Hoto: Nikolai Trishin/TASS/dpa/picture alliance
Miliyoyi sun yi gudun hijira
Yakin na Ukraine ya janyo kwararar 'yan gudun hijira a kasashen Turai, wanda ba a taba gani ba tun yakin duniya na biyu. Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNCHR ta ce, zuwa watan Fabarairun 2023 'yan gudun hijirar Ukraine a Turai sun fi miliyan takwas. Poland ta karbi sama da miliyan daya da dubu 500. Miliyoyi daga yankin gabashi da kudanci, sun watsu a sassan kasar.
Hoto: Anatolii Stepanov/AFP
Karbe iko da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia
A makon farko na mamayarta, Rasha ta karbe iko da yankuna da yawa a kudanci da gabashin Ukraine da ma wani bangare na arewaci musamman kusa da birnin Kyiv. Tun daga wannan lokaci, babbar tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia da ke yankin kudanci ke karkashin ikon Rasha. Yakin ya shafi farfajiyar tashar. Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa IAEA ta ce a sanya shingen kariya.
Hoto: Str./AFP/Getty Images
Ba a san adadin wadanda suka rasa ransu a yakin ba
Babu wanda ya san adadin wadanda suka rasa rayukansu a yakin. Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kimanin fararen hula dubu bakwai da 200 da kuma sojoji dubu 12 sun halaka. Sai dai ta ce, adadin ka iya fin haka. Ba a san yawan sojojin Ukraine da suka halaka ba. A watan Disamabar bara, mai bai wa shugaban kasar shawara Mykhailo Podoljak ya ce sun kai dubu 13. Sai dai babu tabbaci kan adadin.
Hoto: Raphael Lafargue/abaca/picture alliance
Tashin bama-bamai a gadar Crimea
A farkon watan Oktbar 2022, an samu tashin bama-bamai a gadar yankin Crimea da Rasha ta mamaye. Bama-baman sun lalata wani bangare na gadar da fadar Kremlin ta gina, a kan titin Kerch. Rashan dai ta ce, wata mota ce makare da bama-bamai daga Ukraine ta tashi a gadar. Sai dai tuni mahukuntan Kyiv suka mjusanta wannan zargi.
Hoto: AFP/Getty Images
Munanan hare-hare a tashar samar da hasken wutar lantarki
Kwanaki kalilan bayan tashin bama-bamai a gadar Crimea, Rasha ta kai mummunan hari na farko a kan tashar samar da hasken wutar lantarki. Matsalar ta fi shafar biranen Lviv da Kharkiv. Tun daga lokacin, harin ya zama na yau da kullum. Saboda mummunar barnar da harin ya yi a tashar, kusan a baki daya Ukraine ana fama da rashin hasken wutar lantarki ko ruwa ko kuma abin dumama daki a kowacce rana.
Hoto: Genya Savilov/AFP/Getty Images
Yaki da kuma sajewa cikin kasashen Turai
Volodymyr Zelenskyi na aika sakon faifen bidiyo a kullum tare da bayyana halin da kasar ke ciki, kuma miliyoyin mutane na kalla. Shugaban ba wai daga al'ummar kasarsa Ukraine kadai ba, ya ma samu taimakon daukacin kasashen yammacin duniya. A karkashin jagorancinsa, sajewa da kasashen Turai ya kai wani matsayi. A yanzu, Ukraine na neman zama mamba a kungiyar Tarayyar Turai EU.
Hoto: Kenzo Tribouillard/AFP
Ukraine na fatan samun motocin yaki kirar Leopard-2
Yadda Ukraine za ta iya karawa da Rasha, ya dogara ne ga taimakon da za ta samu. Kasashen kawance karkashin jagorancin Amurka, na samar da miliyoyin dalar Amurkan ga fannin tallafin jin-kai da kudi da kuma sojoji. An tafka gagarumar muhawara kan aika manyan makamai, a tsakanin kasashen Yamma saboda tsoron matakin da Rasha za ta dauka. Amma Ukraine na son samun manyan tankokin yaki kirar Leopard-2.
Hoto: Ina Fassbender/AFP/Getty Images
Hotuna 91 | 9
A jawabinsa shugaban Rasha Vladimir Putin da ke zaune a tsakiyar wasu tsofaffin shugabannin kasashen tsohuwar Tarayyar Soviet, ya nemi nuna karfin tasirin Rasha ta fuskar makamai. Putin ya ci alwashin sai sun sami nasara a kan Ukraine yana mai cewa: "Kasashen yammacin duniya har yanzu suna nuna sun fi kowa, suna gwara kan mutane da raba tsakanin al'umomi da tunzura zubar da jini da juyin mulki da kuma dasa kiyayya a zukatan al'umma da kuma nuna kyamar Rasha. Girman kansu da shisshigi sun haifar da bala'i, wannan shi ne dalilin masifar da mutanen Ukraine suke fuskanta a yanzu kuma sojojinmu za su yi nasara."
Jawabin na Putin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kamfanin sojin haya na Rasha Wagner ya zargi sojojin Rashan da guduwa daga filin daga a Bakhmut, inda ake tsakiyar barin wuta a Ukraine. Wagner sun shafe watanni suna jagorantar fafatawa a Bakhmut, yankin masana'antu da ke gabashin Ukraine da yakin ya daidaita. Sojojin Rasha ba su tabuka wani abin a zo a gani ba, yayin yakin da suka gwabza a lokacin sanyin hunturu. A hannu guda kuma shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta tashi daga Poland zuwa Kiev, inda ta gana da shugaban Ukraine a kokarin kasarsa na shiga kungiyar ta Tarayyar Turai. A nasa bangaren shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa daga yanzuu kasarsa za ta rika yin bikin wannan rana a matsayin ranar nasara ga Tarayyar Turai. Ya kuma bukaci kungiyar ta EU ta hanzarta shigar da kasarsa cikinta.