1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bill Clinton zai ba da da shedar alakarsa da Epstein

Abdul-raheem Hassan
February 27, 2026

Tsohon Shugaban Amurka din ya yi ta amfani da jirgin saman Epstein a farkon shekarun 2000 bayan da ya kammala wa'adin mulkinsa, kuma an ga hotunansa da 'yan mata a Epstein files.

Tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton
Tsohon shugaban Amurka, Bill ClintonHoto: SAUL LOEB/AFP

Clinton zai bayyana a gaban kwamitin jin bahasi don fayyace gaskiyar dangantakarsa da Jeffrey Epstein, wanda ake zaregi da yin kawalci da kanaan yara, bayan da matarsa kuma tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta fadawa majalisar wakilai cewa ba ta taba mafarkin haduwa da Epstein ba kuma babu abin da ta sani gaame da laaifukansa na cin zarafi.

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta bankado yadda aka ga hotunan Bill Clinton da wasu 'yan mata da sukaa sauya fuskokinsu, amma Clinton ya nesanta kansa da aikata wani laifi tare da nadamar alaka da Epstein. Shugaban kwamitin jin bahasin daga jam'iyyar Republican, James Comer na Kentucky, ya ce ba a zargin Clintons da aikata ba daidai ba amma dole ya amsa tambayoyi game da alakar Epstein da gidauniyar agajinsa.

Sun amince da bada shaida a kusa da gidansu na Chappaqua da ke birnin New York, bayan da majalisar wakilai ta yi barazanar kama su da laaifin raina majalisa na kin ba da hadin kai. Wasu 'yan jam'iyyar Democrat sun goyi bayan matakin.

Clinton da matarsa sun zargi 'yan Republican da nuna bangaranci da siyasa don kare Shugaba Donald Trump daga bincike, lura da cewa wasu a cikin binciken an yarda su gabatar da bayanan da aka rubuta maimakon yin shaida gaba da gaba. 'Yan jam'iyyar Democrat sun ce ya kamata kwamitin ya kuma gayyaci Trump, wanda sunansa ya bayyana akai-akai a cikin takardun da ke da alaka da Epstein.

Trump ya yi alakar kud da kud da Epstein a 1990s da 2000, kafin kotu ta same shi da laaifin lalata da kananan yara a shekarar  2008. 'Yan jam'iyyar Democrat suna zargin ma'aikatar shari'a da boye bayanan wata mata da ta zargi Trump da yin lalata da ita tun tana da karaancin shekaru. Sai dai ma'aikatar shari'ar ta ce tana duba hujjojin tare da nazari kan dacewar wallafa shi.

A baya ma'aikatar shari'ar Amurka ta yi gargadin cewa bayanan da aka saki ya hada da zarge-zarge marasa tushe game da Trump, kuma hukumomi ba su zarge shi da aikata laifuka dangane da Epstein ba.