1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Bincike a gidan Andriy kan zargin cin hanci a Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
November 28, 2025

Jami'an yaki da cin hanci da rashawa na Ukraine na gudanar da bincike kan karkatar da makudan kudade da suka kai dala miliyan 100 a fannin makamashi da ta shafi manyan jami'an kasar, lamarin da ya sa aka kori ministaoci.

Andrij Yermak, a lokacin da ya rufa wa Shugaba Selensky baya a ziyarar da ya kai Spain
Andrij Yermak, a lokacin da ya rufa wa Shugaba Selensky baya a ziyarar da ya kai SpainHoto: Violeta Santos Moura/REUTERS

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Ukraine ta kai samame a gidan Andriy Yermak, da ke zama shugaban ma'aikata ga shugaban kasa Volodymyr Zelensky. Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da fadar mulki ta Kyiv ke tattaunawa da Amurka kan shirin kawo karshen yakin da ke tsakanin Ukraine da Rasha, inda Mista Yermak ya kasance babban abokin hulda kuma wakilin Ukraine a tattaunawar.

A cikin wani sako da ya wallafa a kafar Telegram, Andriy Yermak ya ce masu bincike ba su fuskanci cikas wajen gudanar da aikinsu ba, saboda yana ba su cikakken hadin kai da suka bukata, inda lauyoyinsa ke wakiltarsa.

Jami'an yaki da cin hanci da rashawa ta Ukraine da Ofishin kwararru kan yaki da cin hanci da Rashawa na neman sanin wanda ya karkatar da makudan kudade da suka kai dala miliyan 100 a fannin makamashi, lamarin da ya sa aka kori ministaoci biyu.