1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ana bincikar Betta Edu bisa zargin cin hanci

January 8, 2024

A yayin da ake cigaba da dagun hakarkari bisa jerin zargin cin hanci kan ministar agajin jin kan Najeriya Betta Edu, gwamnatin kasar ta ce ta kaddamar da bincike.

Nigeria Blasphemie Prozess
Hoto: REUTERS

 Wani rikicin cikin gida a tsakani wata jami’ar ma‘aikatar jin kan da ministan bisa batun cin hanci ne dai ke neman rikidewa da mayar da allura garma a ma’aikatar da ta dauki lokaci tana fuskantar zargi. Ana dai zargin Betta Edu da kokari na karkatar da kudaden da suka kai Naira miliyna 585 daga asususn ma'aikatar zuwa asusun wata jami'ar  ma’aikatar na kashin kanta

Shaidun karya na minista Betta Edu a game da kudaden da ta kashe

Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Kuma ko bayan nan dai Edu ta kuma saka hannu tare  da mincewa da wasu kudaden tafiyar da suka hada da tikitin jirgi na sama zuwa Jihjar Kogi a banagre na ministan da jami’anta cikin jihar da ba ta da filin sauka ko tashi na jirage. Tuni dai hakarkari na 'yan kasar ke kara sama cikin kasar da ke fadin a tsuke aljihu, amma kuma jami’anta ke kara nuna alamun shuka dawa a tsohuwar al'adar hanci.

Yunkurin gwamnatin na bin didigin abin da ya faru

Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Zargin dai daga dukka na alamu na shirin ya gigita  Abujarda ke ta laluben hanyoyin tunkarar batun rashin tsrao da tattali na arziki, amma kuma ke kallon cin hanci cikin tafi da harkoki na jami’an da ke tunanin sauyin. Gwamnatin dai ta ce ta kaddamar da binciken da a cewar kakakinta kuma ministan labarai na kasar Mohammed Idris Malagi ke da babban burin tabbatar da gaskiyar abun da yafaru.