Bincike kan hari a Indiya
July 14, 2011Talla
A ƙasar Indiya ana nan ana gudanar da bincike akan hare-haren bom da aka aiwaitar ranar Laraba 13 ga watan Yuli da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 17. Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadar da hare haren da aka ƙaddamar a wata cibiyar kasuwanci da ke kudancin birnin Mumbai. Wasu kuma su 40 sun samu raunuka. Shekaru biyu da rabi kenan da wasu 'yan bindiga da ake zaton daga Pakistan suka fito suka aiwatar da hare-hare a wannan wuri. Babu dai wata ƙungiya da ta yi iƙirarin kai wannan hari. Amma ministan cikin gidan Indiya ya faɗa wa manema labarai cewar 'yan ta'adda ne ke da alhakin wannan hari.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu