1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramta taliyar indomi a Najeriya

Muhammad Bello
May 2, 2023

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta NAFDAC ta fara wani bincike kan zargin cewar akwai hadari ga cimakar Indomi da ta riga ta zama abinci a Najeriya.

Indonesische Produkte in Deutschland
Taliyar Indomi ta IndonesiyaHoto: DW/A. Purwaningsih

Satin da ya gabata dai wasu kasashen duniya sun bayyana damuwa kan cewar taliyar ta Indomi da a ke safarar sa daga kasashen ketare na tattare da wani sinadari da ke jawo cutar daji ta Cancer.

Tuni dai wannan al'amari ya jefa miliyoyin 'yan Najeriya ma su kasuwancin na Indomi da kuma ma su ci cikin damuwa da kuma rudanin ko wace makoma ke nan in har ba Indomi, musamman ma ganin hukumomi a Najeriya sun ce hatta Indomi din ma ta gida Najeriya za'a bincike ta.

Ganin dai yadda wasu kasashen duniya suka bayyana matukar damuwa kan cewar cimakar ta Indomi da ake safarar ta musamman daga kasashen Taiwan da Malasiya na dauke da sinadari da a ke kyautata zaton na haifar da cutar daji ta Cancer.

Hukumar ta NAFDAC  dai ta ce da man cimakar ta Indomi na a jerin abincin da ta hana shigowa da su daga kasashen ketare.

Taliyar Indomi daga kamfanin Indofood a IndonesiyaHoto: Getty Images/AFP/B. Ismoyo

Da haka hukumar ta NAFDAC ta ce ba a da bayan sa Ido yanzu sosai, wajen ganin ba a sake shigowa da Indomi din ba daga kasashen waje, ta ce a yanzu ya zama wajibi ta fara binciken kwakwaf kan Indomi ta gida da miliyoyin 'yan Najeriya su ka mayar abinci na kusan ko da yaushe.

Wata Elizabeth Hart da kan ci Indomi a kullum ta ce:

"Ina cin Indomi a ko da yaushe, kuma jin wannan labari na Indomi na haifar da Cancer ya tayar min da hankali."

Wannan gaba dai da ake kai yanzu daga dukkanin alamu bai yi wa da daman 'yan Najeriya dadi ba gami ma da ma su cinikin na Indomi a kullum.

Peter Oke Chukwu wani mai kanti a birnin Fatakwal kuma ke sayer da Indomi ya ce:

"Indomi da ka ke gani fa ta zama abinci ga 'yan Najeriya, kuma yanzu in ba ita to rayuwa za ta gigita, yara da manya kowa da kowa na cin Indomi, na kan sayar da katon 40 ko fi a kantina duk satin Allah. Don haka tsaiko a cimakar Indomi tamkar bai wa yunwa kafa ne ta afko cikin kasa."

Binciken kwararru dai ya nuna cewar an gano sinadarin Ethylene Oxide a tattare da taliyar ta Indomi Noodle, da kuma  ba makawa ke haddasa cutar ta Cancer, kuma kan binciken da NAFDAC din tara, ta ce za ta sanar da 'yan Najeriya sakamakon bincike nan ba da dadewa ba.

Yahaya Archibong na sana'ar dafa Indomi da kwai da shayi safe da rana da dare, a bakin masallacin da ke kan titin Niger Street, a Fatakwal.

Sinadran hada taliyaHoto: Getty Images/AFP/D. Dutta

Ya ce "Na kan dafa wa jama'a Indomi babba da ake kira Hungry Man, akwai kuma SuperPack, shima babba, sai kuma karami".

Sai dai kuma kamfanin na Indomi mai suna INDOFOD da ke Indonesia, na ci gaba da kafewar cewar, taliyar Indomi da ta ke samarwa don amfanin kasashen duniya daban daban yau sama da shekaru 30, lafiya kalau ta ke, kuma ta cika dukkanin wasu kaidoji na kiyaye lafiyar jamaa.

Binciken masana dai tun ba yanzu ba, ya nuna cewar yawan dibgar shinkafa, da taliyar Indomi da Biredi, na kara hadarin kamuwa da mugunyar cututtuka irin su Cancer da ciwon sikari ko Diabetis, gami da hawan jini, da kassara mafitsara, sai shanyewar rabin jiki da kuma kiba ta cuta.