Binciken kisan Fulani a kasar Burkina Faso
January 8, 2023Talla
Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi da a gaggauta gudanar da bincike kan kisan wasu mutane 28 da aka yi a garin Nouna da ke arewa maso yammacin kasar Burkina Faso. A karshen watan Disambar da ta gabata, aka gano gawarwakin mutanen a garin da akasarin mazaunan yankin suka kasance Musulmai kuma 'yan kabilar Fulani.
Shugaban hukumar Volker Turk, ya baiyana gamsuwarsa kan matakin da majalisar ta dauka, yana mai cewa, cike ya ke da fatan ganin an yi adalci tare da fayyace gaskiya kan abin da ya faru a Nouna da ya kuma yi sanadiyar mutuwar wadannan mutanen.