1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike ya ce kamfanonin makamai sun samu gagarumar riba

December 1, 2025

Wani sabon rahoton bincike, ya tabbatar da yadda kamfanonin kera makamai na duniya suka samu makudan kudade a bara, lamarin da ke da nasaba kai tsaye da yake-yaken da ake gani a duniya da ma sauran matakai.

Rasha | Wani Makamin Roka na Iskander
Rasha | Wani Makamin Roka na IskanderHoto: Russian Defense Ministry Press Service/AP Photo/picture alliance

Kamfanonin kera manyan makamai a duniya, sun samu karuwar kudaden shiga da kaso 5.9 cikin ɗari a bara, sakamakon karuwar bukatu da ta samo asali daga yakin Ukraine da Gaza, tare da karin wasu kashe-kashen tsaro da kasashe ke yi.

A cewar rahoton da cibiyar binciken neman zaman lafiya ta kasar Sweden SIPRI, ta fitar a wannan Litinin, kudaden shiga da manyan kamfanoni 100 masu kera makamai suka samu sun haura zuwa dala biliyan 679 a 2024, adadi mafi yawa tun da aka fara irin wannan kididdiga a duniya.

Yawancin wannan karuwa ya fito ne daga kamfanonin kasashen Turai da na Amurka, duk da cewa an samu dan karuwa a sauran nahiyoyi, banda Asia da Oceania, inda matsalolin da ke tattare da masana’antar makaman China suka janyo raguwar kudaden shiga.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW