Illar abincin gwamgwami ga yara
December 3, 2025
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya bayyana cewa kananan yara a duniya na cin abincin gwangwani da aka sarrafa da abubuwan da ke da illa a jikin dan Adam fiye da kima. Cikin wani sabon rahoto da asusun ya fitar ya ce, irin wadannan abinci da yara ke ci, na da matukar illa ga girman jikinsu da ma lafiyar kwakwalensu.
Binciken da aka yi
Rahoton ya ta'allaka ne da wani bincike da mujujallar kiwon lafiya ta The Lancet ta gudanar, wanda ya yi bayani dalla-dalla kan illolin da wadannan abincin gwangwani da aka sarrafa ke da su da mafi akasari suke dauke da siga da gishiri da kuma kitse da ke da illa ga lafiyar dan Adam.
Binciken da aka gudanar a wasu kasashe 11, ya nunar da cewa matsalar na shafar kaso 10 zuwa 35 na kananan yara 'yan shekaru biyar, yayin da ya kunshi kimanin kaso 60 cikin 100 na matasan da ke tasowa.