1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

WHO ta fara gano asalin corona a China

January 29, 2021

A wannan Jumma’a kwararru daga hukumar lafiya ta duniya WHO, sun fara aikin gano asalin kwayar cutar corona a birnin Wuhan na China.

China | Corona | Virusausbruch | Ermittler
Hoto: Ng Han Guan/AP Photo/picture alliance

Wannan na zuwa ne bayan makonni biyu da suka yi a killace bisa dokokin corona na China. Rahotanni na nuna cewa tuni har jami'an na WHO suka fara ganawa da hukumomin China domin fara bincike a kan asalin corona wace ta zamar wa duniya alakakai.

WHO ta sanar a shafinta na Twitter cewa jami’an nata za su tattauna da mutanen farko da suka fara kamuwa da corona a China sannan za su shiga kasuwar namun dajin da ake zargin daga nan aka fara samun bullar coronar sai kuma wasu dakunan bincike na kasar ta China. WHO ta ce tana fata jami'an nata za su samu cikakken goyon baya a yayin da suke fara wannan gagarumin aiki.