1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali tana binciken kisan fararen hula

Suleiman Babayo MAB
April 7, 2022

A kasar Mali da ke yankin yamamcin Afirka sojojin kasar sun kaddamar da bincike bisa zargin kisan da aka yi wa fararen hula a garin Moura na yankin tsakiyar kasar.

Mali Oberst Assimi Goita, Anführer der malischen Militärjunta
Hoto: Annie Risemberg/AFP/Getty Images

Kasar Mali ta bayyana cewa sojoji masu binciken sun kaddamar da neman sanin hakikanin abin da ya faru a kauyen Moura a ke zargin aikata kisan kare dangi. Mai gabatar da kara na soja ya ce bayan zargin cin zarafin fararen hula da aka samu, hukumomi sun kaddamar da bincike.

A farko wannan wata na Afrilu sojojin Mali sun bayyana halaka tsageru 203 a garin na Moura, amma daga bisani rahotanni daga kafofin sada zumunta na zamani suka nunar da cewa kisan kare dangi sojojin suka aiwatar.

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch ta ce sojojin Mali da mayakan kasashen ketere sun halaka fararen hula kimanin 300 a Moura. Rasha take samar da abin da ta kira masu horas da sojoji ga kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka. Sai dai kasashen Amirka da Faransa gami da wasu kasashe sun ce masu ba da horon sojojin hayan ne na kamfani mai zaman kansa na Wagner na kasar ta Rasha.