NATO: Kyautar bindiga daga Erdogan
July 9, 2026
Mai masaukin baki Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya yanke shawarar rabawa shugabbin kasashen kawancen na NATO kyautar wata 'yar karamar bindigar hannu samfurin Gumusay .357 Magnum da kuma harsasai masu rai.
Mamaki bayan ganin kyauta
Firaministan kasar Beljiyam Bart De Wever ya sha mamaki lokacin da ya isa gida ya kuma ga bindigar cikin kayansa, inda tuni ya mika ta ga jami'an tsaron filin jirgin sama na Brussels don a alkinta ta. Ofishin shugaban kasar Lithuanian Gitanas Nauseda ya fitar da wasu hotuna, dauke da dan karamin akwatin kyaututtuka da aka zana tutar Turkiyya da tambarin NATO da kuma bindigar da aka rubuta Gumusay a jikinta.
Kakakin firaministan Spaniya Pedro Sanchez ya ce, an bai wa duka shugabannin kasashen wannan kyauta ta bindiga da kowa aka rubuta sunansa a jikin tasa. Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, za ta bayar da tata ga gidan adana kayan tarihi na sojoji. Bindigar dauke da makamai masu rai, na nuni da cewa ba an bayar da ita ba ne saboda kwalliya.
Kyauta ko talla cikin dabara?
Masana na ganin cewa, Turkiyya na son yin amfani da wannan dama ta nuna karfin da take da shi wajen kera kananan makamai. Ankara ce dai kasa ta uku da ta fi fitar da kanan makamai a tsakanin shekarun 2019 zuwa 2024, kamar yadda wani binciken wata cibiya kan kananan makaman da ke Geneva ya nunar.