Bio ya zama sabon shugaban Saliyo
April 5, 2018Talla
Sabon shugaban kasar ta Saliyo Julius Maada Bio ya kama aiki gadan gadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.
Bio ya sami kashi 51.8 cikin dari na kuri'un da aka kada inda ya kada abokin takararsa Samura Kamara na Jam'iyyar APC wadda ta shafe shekaru goma tana mulki.
Wanan dai shine karon farko da jam'iyyar adawa ta SLPP ta sami nasarar hawa karagar mulki a kasar ta Saliyo.
Shugaba Julius Maada Bio ya yi alkawarin gudanar da mulki ba tare da nuna banbancin kabila ko addini ba, yana mai alwashin tabbatar da hadin kan 'yan kasa.