1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigakafin corona na yara kanana

Binta Aliyu Zurmi MNA
April 29, 2021

Kamfanonin BioNTech da Pfizer na shiriye-shiryen karshe na fidda da rigakafin cutar corona ga yara masu shekaru 12 zuwa 15 nan da watan Yuni a kasashen Turai.

Türkei Pfizer BioNTech Ampullen
Hoto: Abdurrahman Antakyali/Depo Photos/ABACAPRESS/picture alliance

Shugaban kamfanin BioNTech, Ugur Sahin, ya ba da wannan sanarwa a tattaunawar da ya yi da mujallar nan ta "Der Spiegel" da ke Jamus. Sanarwar ta kara da cewa za su jira hukumar da ke tantance ingancin magunguna a Turai ta ba da amincewarta, binciken da ake ganin zai dauki makwanni hudu zuwa shida.

Yanzu haka dai duka kamfanonin na kokarin ganin an amince da rigakafin nasu da za a iya yi wa kananan yara tun daga wata shida zuwa sama.

Ana ganin saka yaran a jerin masu karbar rigakafin zai taimaka wajen kawo karshen annobar da ma bai wa yaran damar ci gaba da karatunsu kamar yadda ya kamata bayan da suka kwashe tsawon lokaci suna karatu daga gida.