1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samar da rigakafin corona ta yara

September 20, 2021

Kamfanonin harhada magunguna na BioNTech da Pfizer sun ce sun samar da allurar rigakafin cutar coronavirus da ke da tasiri ga yara 'yan shekaru 5 zuwa 11.

Coronavirus - Impfung beim Kinder- und Jugendarzt
Hoto: Fabian Sommer/dpa/picture alliance

Kamfanonin biyu za su mika bayanan gwaji kan allurar ga hukumomin kasashen Turai da Amirka da ma wasu kasashen nan bada jimawa ba. Za a fara gwajinta kan yara kimanin dubu 2 da dari 2 kuma ake sa ran su fuskanci wasu alamomi na kumburin hannu da dai sauransu bayan karbar allurar fiye da manya. 

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da ake samun yaduwar cutar tsakanin yara a kasar Amirka da ma wasu sassa na duniya. Tuni dai hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amirka FDA ta amince da rigakafin annobar ta yara ta Kamfanin BioNtech yayin da sauran kamfanoni irinsu Johnson & Johnson da Moderna sun fara gudanar na su gwajin rigakafin na yara.