1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birnin Legas cunƙus ɗakin tsumma

January 21, 2011

Birnin Legas cibiyar hada-hadar kasuwanci a tarayyar Najeriya ya shiga jerin manyan birnen duniya da akewa laƙabi da Mega Cities, musamman dangane da girmansa da yawan al'umma daban daban da ya ƙunsa.

Legas birni dake ƙara haɓakaHoto: DW

Shirin na mu na yau ya samu zantawa da Sefi Atta, marubuciya kuma ‘yar birnin Legas wanda a tsakiyar shekarun 1990 ta ke ƙasar Amirka amma ta na yawaita kai ziyara gida kuma ta shaida irin canje canje da Legas ta samu. Akan haka Sefi Atta marubuciyar adabi ce wadda a rubuce-rubucenta ta kan yi nuni da yanayin zamantakewa a birnin Legas. A shekarar 2009 ta samu kyautar NOMA ta adabin Afirka akan littafinta mai taken Labarun Gida, wato News From Home. A shekarar 2008 an fassarar littafinta na farko kan birnin Legas mai taken “Everything Good will come” a cikin harshen Jamusanci. Ga dai bayani wani sashe na wannan littafi.

Sefi AttaHoto: DW

“Yana da wuya ka so wannan birni. Kasuwanci a yamutse. Ciniki na bunƙasa a gefen hanya, a shaguna, a kan masu talla, a unguwannin wajen gari, inda aka canza fasalin gidajen mutane izuwa cibiyoyin hada-hadar kuɗi domin ya dace da buƙatunsu. Sakamakon haka shi ne datti da tulin shara a kan tituna, a cikin magudanar ruwa da kasuwanni.”

Enitan da Sheri su ne mata matasa biyu da Sefi Atta ta bi diddigin rayuwarsu a littafin na ta. To amma suke rayuwa nesa da hayaniya da datti da suka zama ruwan dare akan titunan unguwannin dake wajen Legas. Ita dai Sefi Atta wadd aka haife ta a shekarar 1964, ‘yar unguwar Ikoyi ce da ta taɓa kansancewa unguwar turawan mulkin mallaka, kana bayan ‘yancin kan Najeriya a 1960, ma'aikatan gwamnati da ‘yan siyasa da kuma ‘yan kasuwa suka maye gurbinsu.

Tuƙin ganganci ba sabon abu ba ne

Yawan ababan hawa na gurɓata iskaHoto: DW

Cunƙoson motoci kenan a rawul wato round-about ɗin Falomo da ke akan titin Awolowo dake zama ruhin unguwar Ikoyi. Sefi Atta ta tuna da wannan yankin da ke zama cibiyar kasuwanci ta Falomo da cewa a lokacin aikin ginin a shekarar 1975, mazauna unguwar sun nuna fargaba game da cunƙoson motoci da wannan aikin sabunta unguwar zai haddasa. An gina babbar gada dake shiga unguwar Victoria Island cibiyar bankunan birnin Legas.

“Mun yi murna lokacin da ake aikin gina gadar. Na kan bi kai ko da ƙafa ko a keke domin kaiwa abokanne na ziyara a unguwar Victoria Island. Amma yanzu ba za ka iya bi ta kai da ƙafa ko a keke ba. Ni kam ba zan yarda ɗa na yayi haka. Amma hakan ba matsala ba ce a da.”

Hatta da mota ma sai mutum yayi da ƙyar wato sai ya bi cikin go-slow kafin ya isa Victoria Island wadda gadoji biyu suka haɗeta da Tsibirin Legas wato Lagos Island, inda unguwar Ikoyi take. A bayan bankunan da ƙasaitattun otel-otel ana iya hango igiyar ruwa a tekun Atlantika musamman a bakin teku na Bar Beach.

Wurare masu kyau duk da ƙazanta

In kunne ya ji gangan jiki ya tsiraHoto: DW

Sefi Atta ta yi mamaki yadda har yanzu ruwan ke da launin shuɗi sannan rairayin kuma na nan fari. Ga al'umar Legas wannan wurin ya kasance wani wuri na musamman, inda a kowace ranar Lahadi bayan coci su kan je don shaƙatawa a bakin teku. Amma a yau wani allo da aka kafa a sabon wurin ya haramta yin ninƙaya a nan.

“Bakin tekun na da hatsari. Idan ba ka wani ɗan'uwa da ruwa ya ci shi, to wataƙila ka taɓa samun labarin wanda ruwa ya ci shi. A shekarun 1970 wannan wuri ya kasance wurin harbe ‘yan fashi da makami wato Firing Squad. Har yanzu ina tune da wannan lokaci. Ina kuma tunawa da bakin tekun a matsayin wani wuri mai ban tsoro da firgitarwa.”

Wasu shingaye na duwatsu da kankare suka raba hanyar titi da bakin tekun. Wasu shekaru ƙalilan da suka gabata an samu zaizayewar ƙasa a wannan wuri abin da ya yi barazana ga gidajen masu hannu da shuni na unguwar. Bangon kankaren na janyo hankali da cewa Legas wani yanki ne da ruwa ya kewaye shi kuma kullum yake fuskantar barazanar ambaliya.

Unguwar masu hannu da shuniHoto: DW

Na gwamna masu gida rana

A Ikoyi musamman a unguwar Fashore Estate ta masu hannu da shuni kana iya ganin manyan gidaje masu kyakkyawan ginshiƙai salon na gine-ginen mutanen Girika. Ko wane fili yana da katafaren bango da aka kewaye samansa da wayoyi masu ƙaya.

“Kowa a Legas na ƙoƙarin ginawa kansa wata fada. Saboda rashin wutar lantarki da rashin ruwan fanfo, su da kansu ke samarwa kansu waɗannan abubuwa har da ma tsaro. A cikin littafi na na ɗan barkwanci da cewa kowa na ginawa kansa ‘yar ƙaramar janhuriya. Idan kana da hali sai ka saye ta ka.”

Ƙarar jenereto da cunƙoson ababan hawa da yanayin kasuwannni abubuwan da aka saba da su ne a Legas, kamar a wannan kasuwar dake unguwar Obalende dab da babban barikin soji.

Kayan abinci ba sa ƙaranci a kasuwar ObalendeHoto: DW

A kasuwar kaji da sauran dabbobi da kuma kayan lambu da dai sauran kayakin buƙatun yau da kullum. Motoci da babura da ‘yan amalanke da masu ciniki ke kai komo a kasuwar. Duk da cewa Sefi Atta ta saba da yanayin manyan kantuna a Amirka, amma tana jin daɗin yanyin kasuwar ta Legas inda komai yake a yamutse.

“Dole ƙwaƙwalwarka ta yi kaifi, domin matan kasuwa sun iya ciniki ƙwarai da gaske. Suna ganewa idan kai ɗan gari ba ne. Hatta ni ɗin nan ma suna iya banbanta ni saboda kayan da na sa. Ko da kuwa irin kayan sawa na gargajiya ne, za su iya ganewa, kuma za su iya amfani da wannan damar domin su cuce ni ko kuma in ce su sha gaba na.”

Sabon rukunin matasa ma'aiakata

Duk matashi mai aiki na dindindin ba zai je wannan kasuwa ba inji Sefi Atta. Domin ɗaukacin matasa masu matsakaicin hali sun gwammace su yi cefa ne a manyan kantuna masu injunan sanyaya ɗaki duk da cewa a can kaya sun fi tsada.

Legas wani babban birnin ne dake canzawa. Unguwannin talakawa na cakuɗe a tsakanin sabbin gine-ginen bankuna. Sabuwar gwamnatin birnin ta kwashe shara daga tituna, ta ta da ‘yan tireda daga bakin titi, kana ta ɓullo da sabon tsarin sufuri. Ko shin Legas za ta ci-gaba da haka? Sefi Atta ta nuna shakkunta.

“Akwai wani karin magana da ke cewa “Eko o ni baje” wato Legas ba za ta taɓa lalacewa ba. Fata na dai shi ne mu mutanen Legas, ba za mu lalata ta ba. Amma yadda na ga abubuwa suna canzawa, to wallahi fata na kaɗan ne. To sai dai duk da haka, ina da dalili na yin kyakkyawan fata. Wataƙila domin ba mu da wani zaɓi face mu ci-gaba da yin fata na gari.”

Mawallafi: Thomas Mösch / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu