An tsoratar game da rashin zuwan yara makaranta a Birtaniya
June 9, 2020Talla
Tun da fari sai da gwamnati ta daukarwa iyayen yara alkawarin bude makarantun firamare a wannan lokaci bisa sharadin bayar da tazara tsakanin dalibai, batun da kungiyar malaman makaranta ta yi na'am da shi kodayake wasu daga cikin 'yan jam'iyyar firaiminista Johnson sun soki shirin bude makarantun.
A nasa bangaren shugaban kwamitin ilimi a Majalisar Dokokin kasar Robert Halfon tsoratarwa ya yi game da yadda wasu yara ke zuwa makaranta yayin da wasu suke zaune a gida ba sa samun damar daukar darasi ta kafar Internet saboda iyayensu masu karamin karfi ne. Yanzu haka dai kididdigar da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar ta bayyana kusan mutane dubu 52 ne suka rasa rayuka sakamakon kamuwa da cutar COVID-19.