1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta dorawa Iran harin Saudiyya

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 23, 2019

Birtaniya ta bi sahun Saudiyya da Amirka wajen dora alhakin harin da aka kai wa manyan matatun man fetur na duniya da ke Saudiyya kan kasar Iran.

Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris JohnsonHoto: picture-alliance/ZumaPress/London News Pictures/G. Cracknell Wright

Kafafen yada labaran Birtaniyan sun ruwaito firaministan Birtaniyan Boris Johnson na cewa daga yadda aka kai harin tilas a karfafa zargi kan Iran. Rahotanni sun nunar da cewa Johnson na son ganawa da Shugaba Hassan Rohani na Iran a gefen taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi, da ke gudana a birnin New York na Amirka.

A hannu guda kuma Iran din ta saki tankar dakon man fetur din nan "Stena Impero" mallakar Birtaniyan. Kakakin fadar gwamnatin Tehran ne ya sanar da hakan, inda ya ce tankar na iya ci gaba da tafiya zuwa inda ta nufa. Iran din dai ta kame tare da tsare tankar cikin watan Yulin da ya gabata, bayan da Birtaniya ta kame tare da tsare jirgin ruwan dakon man fetur mallakar Iran din da ke kan hanyarsa ta zuwa Siriya, jirgin kuma da Birtaniyan ta saki tun farkon watan Agustan da ya gabata.