'Yan majalisar dokokin Birtaniya za su koma bakin aikinsu
September 24, 2019Talla
Yanke hukuncin da kotun kolin ta yi dai ya zo ba zato ba tsammani ko da kuwa ga su 'yan adawa kamar yadda aka ji wasunsu na fada. Baki dayan alkalan kotun sun ba da ra'ayin cewar firaministan matakin da ya dauka ya sabawa doka kuma hakan tarnaki ne ga aikin 'yan majalisar dokoki. Shugabar kotun kolin Birtaniya Brenda Hale ta ce: "Wannan kotun ta yanke hukunci cewar shawarar firaministan ta neman izinin sarauniya ya sabawa doka. Hakan na nufin umarnin da ya kai ga rufe majalisar shi ma ba ya kan doka, kuma yanzu bai da tasiri an kuma warwareshi. Hakan na nufin takardan da aka kawo majalisar dokoki na umartan rufe majalisar tamkar farar takarda ce da ba ta da rubutu, rufe majalisar ya tashi daga aiki ."