Birtaniya na bankwana da kungiyar EU
December 31, 2020Talla
Birtaniya ita ce kasa ta farko da ke barin kungiyar mai mambobi 27 da ta kwashe shekaru 47 suna gudanar da ayyukansu tare.
A shakarar 2016 'yan majalisar dokokin Birtaniya suka kada kuri'ar barin EU, wanda aka kwashe shekaru kusan hudu ana tattauna tsarin jadawalin ficewar da kuma makomar dangantarsu da kungiyar EU.
Daya daga cikin kalubalen da alumma a Birtaniya za su fuskanta shi ne na rashin damar shiga kasashen da ke cikin kungiyar tarayar Turai kai tsaye, Kuma a karon farko za a maido da binciken a kan iyakar kasar da kasashen EU.