1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta fara allurar rigakafin corona

Binta Aliyu Zurmi
December 8, 2020

Birtaniya ta fara allurar rigakafin cutar corona a wannan Talatar, kuma za a fara yin rigakafin ne ga wanda suka fi hadarin kamuwa da cutar kamar tsofaffi da masu kula da su da kuma jami'an kiwon lafiya.

UK London | Impfzentrum
Hoto: Dominic Lipinski/AFP

Za dai a fara yi wa mutane kimanin miliyan 20 allurar, hakan ne kuma ya sanya Birtaniya din tanadar alluran guda miliyan 40 don yin amfani da su ga wanda ke sahun farko.

A satin da ya gabata ne Birtaniya ta zama kasa ta farko da ta aminta da alurar rigakafin kamfanin Pfizer da na BioNtech wanda su ke fatan zai kawo musu karshen wannan annoba da ta addabi duniya. 

Birtaniya dai na daga cikin kasashen da annobar coronavirus ta fi yi wa illa a nahiyar Turai, inda sama da mutum dubu 61 suka rasa rayukansu a kasar yayin da ta ke da sama da miliyan daya da dubu dari shidda na wadanda cutar ta harba.